Manzon musamman na babban magatakardar MDD a Syria Staffan de Mistura, ya ce yana da kwarin gwiwa game da cimma nasarar warware rikicin kasar Sham cikin lumana.
Mr. de Mistura wanda ya bayyana hakan ga 'yan jaridu, jim kadan bayan kammala ganawar sa da wakilan kwamitin tsaron MDD, ya ce mahukuntan kasar Sham, sun alkawarta dakatar da kai hare-hare ta sama, a sassan birnin Aleppo har na tsahon makwanni 6, tun daga ranar da zasu bayyana nan gaba kadan.
A ranar 11 ga watan nan na Fabarairu ne dai Mr. de Mistura ya gana da shugaba Bashar Assad, inda suka tattauna game da shirin da ake yi na tabbatar da nasarar tsagaita wuta a Arewacin birnin na Aleppo.
Kaza lika de Mistura ya gabatarwa shugaban na Sham tsarin dakatar da kaddamar da hare-hare a yankunan fararen hula, a wani mataki na samar da damar shigar da kayayyakin agaji, da kuma komawa teburin shawara.
A nasa bangare shugaba Assad ya bayyana cikakken goyon bayan sa, ga dukkanin wani shiri da zai tallafa wajen kawo karshen rikicin siyasar dake addabar kasar ta sa. Kaza lika ya bukaci daukacin kasashen duniya da su sa hannu, wajen aiwatar da dokar MDD wadda ta tanaji dakatar da samar da kudade da ma dukkanin wani nau'in tallafi ga 'yan ta'adda dake kasar ta Sham.