in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar ISIS na yunkurin mamaye yankunan Sham da Iraqi
2014-07-06 16:54:09 cri

A yanzu haka dai kungiyar nan ta masu tsatsauran ra'ayin Islama ta ISIS, wadda ta sanar da kafa kasar Musulunci mai lakabin "kasar Iraqi da Levant", na ci gaba da mamayar wasu muhimman yankunan hakar mai da iskar gas na kasar ta Sham, a daidai gabar da kuma ta ke kara karfi a sassa daban daban na kasashen Iraqi da Sham.

Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka lardin Deir ez-Zor, dake da muhimmanci a bangaren samar da albarkatun man fetur na kasar Sham na hannun 'yan kungiyar, duk kuma wani yunkuri na kwace wannan yanki da dakaru masu adawa da kungiyar suka yi ya ci tura. Har wa yau an ce wata kungiyar ta daban mai alaka da kungiyar Al-Qaeda a lardin na Deir ez-Zor ta sallama sansanninta, matakin da ya sanya sauran kungiyoyin dake yanki janyewa.

Ban da haka, an ce wasu magoya bayan kungiyoyin tada kayar baya masu karfi dake gabashin Sham, sun bayyana aniyar su ta yin mubaya'a da kungiyar ta ISIS, karkashin jagorancin jigon ta Abu Bakr al-Baghdadi. Wannan dai lamari ya karfafa gwiwar kungiyar wajen kai hare-hare kan sauran yankunan ta Sham, tare kuma da kara karfafa burin ta na kafa sabuwar kasar Islama.

A hannu guda kuma wasu kafofin yada labaru sun bayyana shugaban kungiyar ta ISIS Abu Bakr al-Baghdadi, na gabatar da hudubar juma'a ta cikin wani faifan bidiyo da aka dora a yanar gizo. Faifan ya nuna Al-Baghdadi na bayani a birnin Mosol, birni na biyu mafi girma a Iraqi, inda yake kira ga al'umma su marawa sabuwar kasar da ya ke jagoranta baya.

Sai dai a daya hannun jami'an gwamnatin Iraqi sun musanta wannan bidiyo, inda kakakin harkokin cikin gidan Iraqi ya ce Al-Baghdadi ya jikkata, yayin wani sumamen da sojin gwamnati suka kaddamar, kuma yanzu haka yana jiyya a kasar Sham, don haka faifan bidiyon na bogi ne. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China