Sakatare janar na sa ido tare da nuna damuwa sosai kan dannawar kungiyar IS ta kasar musulunci a Iraki da Levant a yanzu haka a birnin Ayn al-Arab, a arewacin kasar Syria, lamarin da a yanzu ma ya janyo ficewar fararen hula da dama, har ma a kasar Turkiya, kuma an samu mutuwar mutane da wanda suka jikkata da dama, in ji kakakin mista Ban a cikin wata sanarwar da aka fitar a cikin MDD dake birnin New-York.
Sanarwara ta rawaito cewa, kungiyar IS na take hakkin bil'adama da 'yancin kasa da kasa a yayin da take gudanar da kamfenta na ta da hankali.
Birnin Ayn al-Arab, da Kurdawa suka fi rinjaye, wanda kuma aka fi sani da birnin Kobane, ya fuskanci munanan hare-hare daga mayakan IS a makwanin baya bayan nan.
Mayakan IS sun samu nasarar kwace daruruwan kauyukan Kurdawa a kewayen Kobane, lamarin da ya tilastawa miliyoyin jama'a tserewa. (Maman Ada)