Wannan tsokaci dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da kwamitin ya fitar a jiya Juma'a. kaza lika sanarwar ta bayyana cewa tun barkewar rikici a kasar ta Sham, mutane fiye da dubu 220 sun hallaka, kana rabin jama'ar kasar ke gudun hijira. Kazalika al'ummar kasar fiye da miliyan 12.2 na matukar bukatar tallafin jin kai.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, rikicin kasar Sham ya kawo babbar illa ga zaman lafiyar wannan yanki, da ma al'ummonin yankin, da muhalli, da tattalin arzikin kasashen dake da ruwa da tsaki.
A wannan rana, kwamitin ya kira wani taro game da kalubalolin da kasashen dake wannan yanki ka iya fuskanta sakamakon halin jin kai da kasar Sham ke ciki.
Game da hakan wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, yanzu halin jin kai a Sham na kara tsananta, hakan ya sa kasar da ma kasashen dake kewayenta ke matukar bukatar tallafin jin kai .
Ya ce a nata bangare Sin na baiwa jama'ar sham da wadanda suke gudun hijira a kasashen waje tallafin jin kai da kudade. Kana za ta ci gaba da yin hakan a nan gaba gwargwadon bukatunsu. A daya hannun kuma, Sin za ta ci gaba da kara gudanar da hadin gwiwa da kasashen duniya daban daban, wajen sa kaimi ga warware rikicin Sham, ta yadda za a kai ga warware rikicin kasar daga dukkan fannoni. (Amina)