Kwamitin sulhun MDD, ya zartas da wani kuduri dake tir da amfani da makamai masu guba a kasar Sham, yana mai alkawarta bin bahasin wannan lamari da wadanda ke da hannu cikin aiwatar da hakan.
Jim kadan da zartas da kudurin, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya ce kasar Sin na tsayawa tsayin daka, bisa ra'ayinta na kin amincewa da amfani da makamai masu guba a ko wane irin hali.
Mr. Wang ya ce baya ga goyon baya ga kokarin da sassan masu ruwa tsaki ke yi, na aiwatar da kudurorin hukumar yaki da makamai masu guba OPCW, da kuma ayyukan kwamitin sulhu dangane da batun makamai masu guba na kasar ta Sham, kamata ya yi a kiyaye martabar "yarjejeniyar hana yaduwar makamai masu guba", ta kungiyar OPCW.
Har wa yau Mr. Wang ya ce kamata ya yi kwamitin sulhu, ya hada kan mambobinsa, ta yadda za a yi magana da murya guda, domin tabbatar da samun nasarar da manufofin da suka jibanci wannan batu.
Wang Min ya kara da cewa, sabili da haka kasar Sin ta shiga tattaunawa da kwamitin sulhun ya shirya kan kuduri mai lamba 2209, take kuma sa kaimi ga sassan masu ruwa da tsaki daban daban, wajen ganin an cimma daidaito game da matsalar siyasar kasar ta Sham. (Tasallah)