Hukumar sa ido kan hakkin Bil Adam mai hedkwata a birnin London ta ba da labari a jiya Asabar 18 ga wata cewa, kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin kasar Amurka mai yaki da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ya kai hare haren sama a gabashi da arewacin kasar Sham, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula a kalla 5.
Hukumar ta bayyana cewa, hare-haren sun hallaka mutane 3 ciki hadda wani yaro a wata gundumar dake arewacin kasar, kuma mutane 2 a gabashin kasar, yayin da wasu 3 suka jikkata.
An ce, IS da dakarun Kurdistan suna ci gaba da yin musayar wuta a birnin Aynal-Arab dake kan iyakar kasar Sham da Turkiya.
Idan ba a manta ba, IS ta kai hari kan birnin Aynal-Arab dake arewacin kasar Sham kusa da iyakar kasar tun daga ran 16 ga watan Satumba, tare kuma da mamaye garuruwa 'yan Kurdistan da dama, lamarin da ya sa a kalla 'yan gudun hijira dubu 180 ficewa zuwa kasar Turkiya. (Amina)