Kafin a fara shawarwari, Mista Obama ya yi kasaitaccen walima a fadar ta White House, don yin maraba da Mista Xi sannan kuma, shugabannin biyu sun gabatar da jawabansu.
An ba da labarin cewa, shugaban kasar Sin Mista Xi ya fara yada zangon shi na ziyarar aikin kwanaki hudu a Amurkan a birnin Seattle a ranar Talata, sannan daga bisani birnin Washington DC ya kasance zango na biyu.
Ana sa ran daga baya kuma, Mista Xi zai isa birnin New York don halartar taron koli na cika shekaru 70 da kafuwar MDD. (Amina)