A cikin jawabin, Lu Wei ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na dagewa kan tabbatar da tsaron Internet, Sin da Amurka sun dora muhimmanci sosai game da wannan fanni, don haka ya kamata bangarorin biyu su tinkari matsaloli tare, gami da yaki da masu laifuffuka kan Internet.
A wata sabuwa kuma, Mr. Lu ya ruwaito shugaban Xi game da Sin ke tsayawa kan nuna adalci ga dukkan kamfanoni, ciki har da na kasashen waje da ke kasar, kana tana kokarin girmama da kare moriya da hakkinsu.
A nasa bangare, mataimakin ministan kasuwancin Amurka Bruce H. Andrews ya ce, Sin da Amurka manyan abokai ne a fannin tattalin arziki a karni na 21, idan suka gamu da matsaloli da kalubale, ya kamata a yi shawarwari da tattaunawa, ba ya fatan wadannan matsaloli za su kawo lahani game da hadin gwiwar cinikayya tsakanin kasashen biyu.(Bako)