in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an kasashen Sin da Amurka za su ziyarci juna don shirya ziyarar shugaban Sin a kasar Amurka
2015-08-10 13:32:28 cri
Jami'an kasashen Sin da Amurka na shirin ziyarta juna don shirya ziyarar da shugaban Sin Xi Jinping zai kai a kasar Amurka a watan Satumba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne ya bayyana hakan yau a gun taron manema labaru a nan birnin Beijing.

Lu Kang ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun tattauna tare da tsai da kuduri cewa, kasar Amurka za ta tura wasu manyan jami'anta zuwa kasar Sin a watan Agusta da Satumba gabanin ziyarar da shugaba Xi zai kai a kasar Amurka a watan Satumba bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi masa. Yayin da wasu manyan jami'an Sin da abin ya shafa za su je kasar Amurka don shirya wannan ziyarar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China