in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin mu'amala da hadin gwiwa da juna wani babban bangare ne na huldar da ke tsakanin Sin da Amurka
2015-06-28 14:06:55 cri
A jiya Asabar 27 ga wata a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Amurka suna da moriya iri daya ko a tsakaninsu, ko a shiyya shiyya, ko kuma a duk fadin duniya baki daya, a sabili da haka, an fi dora muhimmanci sosai wajen yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A wannan rana, Wang ya fadi haka ne a yayin da yake amsa tambayar da aka bayar game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da bukatar Sin kan manufar da Amurka take dauka kan kasar Sin a gun dandalin tattaunawar kiyaye zaman lafiya a duniya karo na hudu.

Wang ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, dangantaka ce dake tsakanin kasa mai sukuni mafi girma da kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya. Shi ya sa, dangantaka da ke tsakaninsu za ta yi tasiri, ba ma kawai ga wadannan kasashe biyu ba, har ma a duniya baki daya. A kwanan baya, ana ta gabatar da labarai maras kyau dangane da dangantaka tsakanin kasashen biyu. Amma a gun taro karo na 7 na yin shawarwari kan manyan tsare tsare da tattalin arziki da kuma taro karo na 6 na yin shawarwari kan al'adun bil'adam tsakanin kasashen biyu da aka shirya a Washington ba da dadewa ba, an samu sakamako a fannoni sama da 300. Wannan ya sake nuna cewa, Sin da Amurka suna da moriya iri daya ko a tsakaninsu, ko a shiyya shiyya, ko kuma a duk fadin duniya baki daya. Kuma ya nuna cewa, yin mu'amala da hadin gwiwa na da muhimmanci kwarai da gaske a fannin bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Musamman ma shawarwarin da aka yi zasu aza tubali mai kyau ga ziyarar da shugaban Sin Xi Jinping zai kai a Amurka a watan Satumban bana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China