A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Amurka, don haka kasar Sin na son shirya wannan ziyara tare da kasar Amurka, domin samun sakamako mai kyau, ba kawai yadda za a ci gaba da tsara ayyukan hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban ba, har ma,yadda za a ciyar da sabuwar dangantakar manyan kasashen biyu gaba, da kuma nuna kyakkyawar fata ga gamayyar kasa da kasa. Kasar Sin na son ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu gaba a fannonin zuba jari, samun amincewa kan harkokin soja, fuskantar sauyin yanayi, tattalin arziki, kiwon lafiya da makamashi da dai sauransu, haka kuma, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan batutuwan da suka shafi kasar Koriya ta Arewa, da batun nukiliyar kasar Iran da dai sauran harkokin shiyya-shiyya, domin ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen duniya.
A nasa bangare, John Kerrya ya ce, kasar Amurka na son dukufa tare da kasar Sin wajen tabbatar da nasarar ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Amurka, kasar Amurma na goyon bayan kasar Sin kan neman ci gaba da kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar, tana kuma fatan bunkasuwar kasar Sin baki daya. (Maryam)