Dangane da lamarin, yau Jumma'a 26 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron mamema labaran da aka yi a birnin Beijing cewa, al'umma'ar kasar ta Sin su ne suke da ikon fadi yanayin hakkin dan Adam da ake ciki a kasarsu, amma bai kamata kasar Amurka ta koyar da darasin hakkin dan Adam a nan duniya ba. Mr. Lu ya ce kasar Sin na fatan Amurka ta iya kula da harkokin cikin gidanta yadda ya kamata, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin ketare.
Haka kuma Kasar Sin tana son yin shawarwari tare da kasashen ketare bisa akidar adalci da kuma na girmama juna kan batun hakkin dan Adam. (Maryam)