in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari kan batun hakkin dan Adam karo na 19 tsakanin Sin da Amurka
2015-08-16 13:49:06 cri

A ran 13 ga wata, an yi shawarwari kan harkokin kare hakkin dan Adam tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a birnin Washington na kasar Amurka. Kuma bayan taron, bangarorin biyu sun cimma matsayi daya kan yadda aka gudanar da taron ba tare da boye kome ba, kuma aka yi musayar ra'ayi yadda ya kamata, lamarin da ya taimaka matuka ga kasashen biyu wajen karfafa fahimtar juna a tsakaninsu.

A yayin shawarwarin, kasar Sin ta jaddada cewa, idan wata kasa ta zabi hanyar da take bi, bisa halin da kasar take ciki da kuma bukatun jama'arta, bai kamata kasashen ketare su tsoma baki cikin harkokin gidanta ba. Ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su gani yanayin hakkin dan Adam na kasashen yadda ya kamata bisa ka'idojin nuna mutuntawa da adalci, su kuma warware sabanin dake tsakaninsu kan harkokin dake shafar hakkin dan Adam ta hanyoyin yin shawarwari da hadin gwiwa, ta yadda za a iya amfanawa kasashen biyu wajen gina wata sabuwar dangantaka ta manyan kasashe.

Bugu da kari, kasar Sin ta gabatar da wasu tambayoyi ga kasar Amurka dangane da harkokin wariyar launin fata, yin amfani da karfin tuwo da bai dace ba da 'yan sandan kasar suke yi, da kuma leken asirin manyan jami'an ketare da dai sauran harkokin keta hakkin dan Adam da kasar Amurka ta aikata.

Kana bayan shawarwarin, wakilan kasar Sin sun yi taron kara wa juna sani tare da mataimakan 'yan majalisar dokokin kasar Amurka da wasu masanan da abin ya shafa, haka kuma, sun kai ziyara a wani yari dake birnin Montgomery na jihar Maryland ta Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China