Ta ce, kasar Sin ta dade tana fuskantar hare-haren intanet daga katare, lamarin da ya kasance matukar kalubale ga harkokin tsaro da kuma muradun kasar. Don haka, kasar Sin na fatan za a karfafa hadin gwiwa da yin shawarwarin tsakanin bangarorin da abin ya shafa, domin bullo da hanyoyin warware wannan matsala cikin hadin gwiwa.
Bugu da kari, ta ce, kasashen Sin da Amurka su ne manyan kasashen da ke amfani da intanet a duniya, suna da moriya iri daya a fannin tsaron intanet. A saboda haka, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta daina nuna bambanci da kuma nuna wa kasar yatsa kan wannan batu, ya kamata kasashen biyu su fara yin hadin gwiwa kan aikin kiyaye tsaron intanet bisa tushen nuna mutuntawa da amincewa, da kuma yin hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa wajen gina yanayin intanet na zaman lafiya, tsaro, da kuma hadin gwiwa ba tare da wata rufa-rufa ba. (Maryam)