A cikin bayanin, an ce, shugaba Xi, zai kai ziyarar aiki a kasar Amurka, wanda zai shafi makomar dangantaka tsakanin kasashen biyu don moriyar alummar kasashen biyu, kana zai haifar da babban tasiri game da yanayin da ake ciki a duk duniya da ma yankunan shiyya-shiyya.
A cikin bayanin, an ce, sama da shekaru 40 da suka gabata, Sin da Amurka sun karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, kuma an kara cusa sabbin abubuwan da ke cikin wannan dangantaka, kana an kafa tsarin mu'amala daga duk fannoni a tsakaninsu.
Duk da cewa, an samu wasu matsaloli gami da gamuwa da wasu wahalhalu wajen raya dangantakar bangarorin biyu, amma, idan aka bi ka'idar girmama juna, da samun amincewar juna da kawar da sabanni da ke tsakani, za a lalubo bakin zaren warware wadannan matsaloli.
A cikin bayanin, an nanata cewa, shekarar bana, zagayowar shekaru 70 da aka samu nasarar yaki da maharan Fascist, a shekaru 70 da suka gabata, Sin da Amurka sun yi hadin gwiwa kafada da kadafa. Bayan shekaru 70, din ya zama wajibi kasashe biyu sun hada gwiwa tare wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. Raya dangantakar kasashen biyu bai tsaya ga irin moriyar kasashen biyu da ta jama'arsu ba, har ma zai yi amfani wajen kiyaye zaman lafiya da bunkasuwar yankin Asiya da tekun Fasific da duniya baki daya. Zurfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ya kasance wani muhimmin aiki da ke gaban kasashen biyu.(Bako)