Bayanin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun hada kai wajen kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu, wanda hakan ya dace da kiran da Sin ta gabatar game da raya dangantakarsu a sabon yanayi.
A watan Yuni na shekarar 2013, shugabannin kasashen biyu sun yi kwarya-kwaryar ganawa a Annenberg ranch dake kasar Amurka, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani game da wannan kira.
Kiran dai ya kunshi batun kaucewa tada rikice da nuna kiyayya. Na biyu kuma shi ne batun girmama juna. Kana a yi hadin gwiwa wajen cimma samun moriyar juna.
Kasar Amurka dai ta amince da kiran na kasar Sin. Don haka kasashen biyu suka dukufa wajen raya dangantakarsu, ciki hadda fadada hadin gwiwa da warware matsalolinsu yadda ya kamata.
Bayanin ya kara da cewa, koda yake akwai canji kadan game da maganar kasar Amurka a kan kiran a sama da shekara guda, amma duk da hakan Amurka ta jaddada cewa za ta cika alkawarinta na inganta dangantaka tsakaninta da kasar Sin.
Sin ta yi imani cewa, kiran "kafa sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashe" ya bayyana kudurin raya hanyar da ake bi wajen inganta dangantakar Sin da Amurka, kana mai yiwuwa hakan ya samar da kyakkyawar makoma ga dangantakar dake tsakanin kasa da kasa a nan gaba. (Zainab)