in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da kokarin farfado da dangantakar Cuba da Amurka
2015-07-01 19:32:56 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta ce Sin na maraba da yunkurin da ake yi, game da farfado da dangantaka tsakanin kasashen Cuba da Amurka.

Madam Hua ta bayyana hakan ne a ranar Larabar nan. Ta ce wannan mataki ya dace da moriyar kasashen biyu, da ma jama'arsu. Ana kuma fatan Amurka za ta soke takunkumin da ta kadawa Cuba a dukkanin fannoni ba tare da wani jinkiri ba, domin dai bunkasa dangantaka tsakaninta da Cuba, bisa tsarin girmama juna cikin adalci.

Rahotannin na nuna cewa nan gaba a yau ne ake sa ran Amurka za ta shelanta cimma matsaya, game da maido da huldar diplomasiya tsakanin ta da Cuba, tare da kuma sake bude ofisoshin jakadanci tsakanin kasashen biyu.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China