in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta nuna yabo ga ziyarar da shugaban Sin zai kai Amurka
2015-08-26 09:24:20 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka John Kirby ya bayyana a birnin Washington a jiya Talata cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Amurka a wata mai zuwa tana da muhimmanci sosai ga dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. Don haka, kasashen biyu za su yi kokari tare don tabbatar da nasarar ziyarar.

Kirby ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta shirya a jiya Talata, kana ya bayyana cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry yana matukar begen ziyarar da shugaba Xi Jinping din zai kawo.

Kerry ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yayin da yake ziyara a kasar Malaysia a wannan wata, inda bangarorin biyu suka tattauna kan abubuwan dake shafar ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Amurka a wannan karo. Kirby ya bayyana cewa, Kerry zai halarci ayyukan dake shafar ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Amurka.

A gun taron manema labarun, Kirby ya tabbatar da cewa, jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Max Baucus zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 70 da kawo karshen harin Japanawa da za a gudanar a nan birnin Beijing na kasar Sin a ranar 3 ga watan Satumba. Ya ce, Baucus yana begen halartar wannan biki sosai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China