in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da rahoto game da yanayin hakkin bil Adam a kasar Amurka a shekarar 2014
2015-06-26 10:26:35 cri

Yau Jumma'a ranar 26 ga watan nan ne ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fidda rahoto game da yanayin da ake ciki a fannin kare hakkin bil Adam a kasar Amurka na shekarar bara, domin mayar da martani kan makamancin wannan rahoto na sauran kasashen duniya da gwamnatin kasar Amurka ta fitar a kwanan baya.

Rahoton ya bayyana cewa, majalissar harkokin wajen kasar Amurka ta sake fidda wani rahoto game da yanayin hakkin bil Adam a wasu kasashen duniya a jiya Alhamis, inda ta yi sharhi maras tushe kan yanayin da wasu kasashen duniya ke ciki a fannin kare hakkin bil Adam, a maimakon yin da-na-sani, da kuma nuna aniyar kyautata irin wannan mumumman yanayin da ita kanta ke ciki.

Rahoton ya ce, dimbin dalilai sun shaida cewa a shekarar 2014, kasar Amurka wadda ke kallon kanta a matsayin mai kare hakkin dan Adam, ba ta iya shawo kan matsalolin da take fuskanta a fannin kare hakkin dan Adam ba, a maimakon haka, wasu sabbin matsaloli ne ke bullowa a wannan fanni, lamarin da ya tsananta yanayin da take ciki.

Bugu da kari, Amurka ta keta hakkin bil Adam a wasu kasashe ta hanyoyin da ba su dace ba, wanda hakan ya sa ta samun jan kunne sau da dama a yayin tarurukan kasa da kasa kan wannan batu na kare hakkin bil Adama.

Rahoton ya kuma nuna matsalolin da kasar Amurka ke tinkara a fannin kare hakkin bil Adam, kamar batun gazawa wajen dakile amfani da bindiga, wanda ya haddasa matakan nuna karfin tuwo a sassan kasar, tare da kawo babbar barazana ga kariyar hakkin jama'a.

Kaza lika Amurka ta sha azabtarwa, da amfani da hanyoyin da hukumar leken asiri ta Amurka ta kan bi na azabtar da mutane. Haka kuma Amurka ta nuna babban bambanci kan launin fata, inda zuriyoyin 'yan tsirarun kalibu kan sha fama da hakan.

Har wa yau kudi kan jagoranci harkokin siyasar Amurka, don haka da kyar ake iya tabbatar da hakkin jama'a a fannin siyasa. Amurka kasa ce mafi karfin tattalin arziki a duniya, amma ba ta iya ba da tabbaci sosai ga hakkin jama'ar ta a fannin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Kuma ba ta iya tabbatar da hakkin mata, da yara yadda ya kamata ba.

Bugu da kari tsahon lokaci, hukumar tsaron Amurka ta NSA, da sauran hukumomin leken asiri na kasar na sauraron wayoyin shugabanni, da jama'ar sauran kasashe. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China