Ma Kai, ya bayyana hakan ne ranar Jumma'a 25 ga watan nan, yayin ganawarsa da shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso a birnin Brussels, a ci gaba da halartar taron tattauna batutuwan da suka shafi bunkasa cinikayya, da tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu da yake yi. A cewar mataimakin firamiyan kasar ta Sin, baya ga Sin da kasashen dake kungiyar ta EU, hadin gwiwa tsakanin bangarorin Biyu zai matukar taimakawa ci gaban ragowar kasashen duniya.
A nasa tsokaci shugaban hukumar tarayyar Turai Manuel Barroso, cewa ya yi hadin kan bangarorin Biyu na da matukar muhimmanci, don haka ne ma taron na wannan lokaci ya share fagen gudanar babban taron da bangaorin Biyu za su gudanar a birnin Beijing cikin wata mai zuwa.
Taron dai na watan Nuwamba zai zamo irinsa na farko karkashin jagorancin sabbin shuwagabannin kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)