A daren jiya Litinin 1 ga watan Yuli, kakakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen Turai ya ba da wata sanarwa, inda ya nuna cewa, shugaba Herman Van Rompuy ya yi kira ga gwamnatin kasar Amurka da ta yi bincike kan rahotannin game da leken sirri da sa ido da hukumar tsaron kasar ta Amurka ke yi wa hukumomin kungiyar EU, kuma ya bukaci kasar Amurka da ta yi bayani kan lamarin.
A wannan rana kuma, wani kakakin kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya bayyana cewa, bayan da kafofin watsa labarai suka fitar da rahotannin daukar sirri da kasar Amurka ta yi wa ofisoshin kungiyar EU, kwamitin ya fara yin binciken tsaro cikin ofisoshin sa daga duk fannoni.
Bugu da kari, kan lamarin, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana ran 1 ga wata cewa, kasar Faransa ba za ta amince da irin wannan halayya ba a tsakanin kawaye, yana mai bukaci Amurka da ta daina liken asiri nan da nan. Haka kuma Shugaba Hollande ya riga ya yi kira ga ministan harkokin wajen kasar Mr. Fabius da ya yi tuntubar takwaran sa na Amurka Mr. John Kerry don jin bayanin da bangaren Amurka ke da shi kan lamarin. Ban da wannan kuma, minista Fabius zai gana da jakadan Amurka da ke kasar Faransa. (Maryam)