in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron koli na G7 a birnin Brussels
2014-06-05 10:29:26 cri
An kaddamar da taron koli na kungiyar kasashe bakwai masu karfin masana'antu ta duniya G7, wanda kungiyar tarayyar turai ta EU ta jagoranci shiryawa.

Taron dai wanda ya gudana a daren ranar laraba 4 ga wata a birnin Brussels, cibiyar kungiyar EU, ya samu halartar wakilai daga kasashe mambobin kungiyar, in ban da kasar Rasha wanda aka dakatar daga halarta. Wannan ne dai karon farko cikin shekaru 17 da Rashan ta gaza halartar taron kungiyar, wanda ya maida hankali kacokan ga batun halin da kasar Ukraine ke ciki.

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta G7 sun kuma tattauna kan hanyoyin da suka dace a bi wajen sassauta matsanancin halin da kasar ta Ukraine ta fada. Har ma shugaban kwamitin kungiyar EU Jose Manuel Barroso ya bayyana cewa, kasashe mambobin G7 za su yi aiwatar da manufofi guda biyu, wato tattauna yadda za a taimakawa kasar Ukraine wajen tabbatar da zaman lafiya ta hanyar siyasa da tattalin arziki, da kuma matsin lamba ga kasar Rasha, don ganin ta yi watsi da tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar ta Ukraine, tare da daina marawa dakaru 'yan aware na kasar baya.

A nasa bangare shugaban majalisar kungiyar EU Herman Van Rompuy ya jaddada cewa, muddin Rasha ba ta dauki matakan sassauta halin da kasar Ukraine ke ciki ba, kungiyar ta G7 ba za ta sake komawa G8 ba, kana kungiyar EU za ta saka mata sabon takunkumi.

Ban da wannan shugabannin kasashe mambobin G7, da kungiyar EU za su tattauna a fannonin tattalin arziki da cinikayyar duniya, da tsaron makamashi, da sauyin yanayi, da kuma batun bunkasuwa a yayin taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China