A cikin sanarwar, hukumar EU ta ce, alkawarin da shugaba Obama ya yi ya nuna cewa, kasar Amurka ta saurari kulawar da kungiyar EU ke nunawa kan lamarin yadda ya kamata, kuma tattaunawar da bangarorin 2 suka yi dangane da lamarin ta haifar da sakamako.
Har wa yau sanarwar ta ce, alkawarin da Obama ya yi ya taimaka sosai wajen maido da amincewa da juna a tsakanin kungiyar EU da Amurka, sa'an nan ya bude kofar yin tattaunawa a tsakanin bangarorin 2 game da tsara yarjejeniyoyi, dokoki da ka'idoji na bai daya dangane da tabbatar da tsaron bayanai yadda ya kamata.
Haka kuma kungiyar EU na ganin cewa, ana bukatar Amurka ta kara yin kokari wajen tsara ka'idoji kan sa ido kan bayanai da sakonni, wayoyin jama'a, tare da kara tabbatar da tsaron bayanan kasuwanci daga kungiyar EU zuwa Amurka.(Tasallah)