Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria a wannan rana ya rawaito wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta gudanar da hakan ne bisa bukatar kasashen Amurka da Isra'ila, don yaki da aikace-aikacen nuna kiyayya da kasar Lebanon, da sauran kasashen Larabawa ke yi. Jami'in ya kuma nuna cewa, jam'iyyar Hezbollah ta ba da gudummawa matuka ga hadin kan al'ummar kasar Lebanon. Don haka jam'iyyar ta zama abar kaiwa hari daga wasu kasashe da kungiyoyi wadanda ke adawa da ita.
Har ila yau yayin wani taron manema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, kasarsa ita ma ta yi suka ga kungiyar tarayyar kasashen Turai, kan batun shigar da tsagin harkokin sojin kungiyar Hezbollah cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda. (Maryam)