Sin na fatan kara hadin kai da bangarori daban-daban kan batun makamai masu guba na kasar Sham
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sham Madam Hua Chunying ta bayyana matsayin da Sin ke dauka kan batun jigila da lalata makamai masu guba na kasar Sham, a taron manema labaru da aka saba yi a ran 24 ga wata, inda ta nuna cewa, kammala aiki na karshe na sufurin makamai masu guba na kasar ta Sham wata nasara ce da aka samu,kuma Sin tana fatan kara hada kai da bangarori daban-daban da abin ya shafa domin warware batun a siyasance.
Madam Hua tana ganin cewa, a hadin gwiwar, Sin da bangarori daban-daban suna kokarin shiga tsakani ne domin ganin an warware batun ta hanyar siyasa, kuma ta ba da gudunmawarta a fannin tura masana, samar da na'urori, da shiga aikin ba da kariya ga jiragen ruwa dake sufurin makaman. (Amina)