Madam Hua ta nuna cewa, Sin na dora muhimmanci sosai kan sa kaimi ga warware rikicin kasar Sham a siyasance, a ganinta, ya kamata a nace ga ka'idoji biyar, wato warware rikicin ta hanyar siyasa, baiwa jama'ar kasar ikon zaben hanyar da kasar za ta bi nan gaba, tsaya wa tsayin daka kan samun sauyi a fannin siyasa ta nuna hakuri ga bangarori daban-daban, sannan da tabbatar da samun sulhuntawa da hadin gwiwar al'umma, da ci gaba da bin hanyar samarwa sauran kasashen dake kewaye da kasar Sham tallafin jin kai. Muhimmin aikin da aka sa gaba shi ne, sa kaimi ga bangarorin biyu a kasar ta Sham da su zabi hanya mai dacewa da za ta kare moriyar bangarori daban-daban. (Amina)