John Kerry ya nuna ma Ahmad Jarba cewa, yana fatan ganin kungiyarsa mai sasaucin ra'ayi za ta iya taka muhimmiyar rawa a kokarin dakile masu tsattsauran ra'ayi na 'kungiyar kasar Islama ta Iraki da Levant' a kasar Iraki. A nasa bangare, Ahmad Jarba ya ce, tabarbarewar yanayin da ake ciki a Sham da Iraki na bukatar kasashen Amurka da Saudiya su kara ba da goyon baya. Haka kuma, ya nuna rashin jin dadi ga firaministan kasar Iraki Nourial Maliki kan yadda ya kara tsananta rikicin da ake samu tsakanin 'yan darikar Shi'a da masu goyon bayan darikar Sunni a kasar.
Daga bisani, John Kerry ya je fadar sarkin dake Jidda, inda ya gana da sarki Abdullah Bin Abdul-Aziz, sai dai ba abin da aka fitar daga wannan tattaunawa tasu. Amma wasu kafofin watsa labaru sun sheda cewa dalilin ziyarar John Kerry a Saudiya shi ne domin neman kasar ta yi tasiri kan 'yan darikar Sunni dake kasar Iraki, don su shiga a dama da su a sabuwar gwamnatin da za a kafa a kasar Iraki, tare da neman Saudiya da ta kara taka muhimmiyar rawa don dakile kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta 'kasar Islama ta Iraki da Levant'. (Bello Wang)