Bisa rahoton dake kunshe cikin wata takardar sirrin da jaridar mako-mako ta Spiegel ta kasar Jamus ta fitar a ranar 29 ga watan da ya gabata, an ce, hukumar kula da harkokin tsaron kasa ta Amurka ta sanya na'urorin sa ido, da kuma na daukar sirri a hedkwatar kungiyar ta EU, tare da kuma gine-ginen kungiyar da ke birnin Washington, da kuma hedkwatar MDD har tsawon shekaru biyar, a sa'i daya kuma, hukumar tana sa ido kan yanar gizon ginin kungiyar ta EU. Kuma bisa labarin da jaridar ta bayar ran 30 ga watan jiya, an ce, abubuwan da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta yi wajen sa ido kan wayoyi, da kuma yanar gizo na kasar Jamus sun riga sun shallake tunanin al'umma.
Don gane da hakan ne a ranar 30 ga watan Yuni, kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya ba da wata sanarwa, inda ya bukaci kasar Amurka da ta ba da bayani ga kafofin watsa labarai kan rahoton leken asirin hukumomin kungiyar da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta yi. Sanarwar ta nuna cewa, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta riga ta tattauna da hukumomin da abin ya shafa na kasar Amurka da ke Washington, da kuma na birnin Brussels, don tantance bayanan da kafofin watsa labarai suka fitar.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Mr. Laurent Fabius, ya bayyana cewa, kasar Faransa ta riga ta yi kira ga kasar Amurka, da ta ba da bayani kan lamarin, ya kuma ce, idan har rahotanni game da harkokin leken asirin da Amurka ta yi sun tabbata, kasar Faransa ba za ta yafe hakan ba. (Maryam)