Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mista Hong Lei, ya bayyanawa taron manema labaru da ya gudana a Alhamis din nan cewa, gwamnatin kasar Sin na matukar kyamar duk wani mataki da aka iya dauka wanda ya shafi amfani da karfin tuwo kan fararen hula.
Game da tambaya da 'yan jarida suka gabatarwa Mr. Hong kan ko gaskiya ne kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta yi garkuwa da wani Basine? Ya ce Sin na maida hankali kan wannan batu, kuma tana kokarin tabbatar da gaskiyar lamarin. Daga nan sai ya nanata matsayin kasar ta Sin, game da kokarin ta na dakile amfani da karfin tuwo kan fararen hula. (Amina)