An ce dakarun Amurka sun yi luguden wuta ta sama a jihar Nangarhar dake gabashin kasar, lamarin da ya sabbaba kisan jagoran na IS.
Ita ma hukumar tsaron kasar Afghanistan ta bayyana cewa Gül Zaman, da sauran mambobin kungiyar IS guda shida sun rasa rayukansu a sakamakon hare-haren da jirgin sama maras matuki na kasar Amurka ya kaddamar. Ko da yake ba ta bayyana hakikanin lokacin da aka kaddamar da hare-haren ba. (Zainab)