Wata sanarwa ta rawaito Carter na cewa a daren ranar Juma'a, bisa umurnin da aka ba su, sojojin Amurkan sun harbe Sayyaf a wani wuri dake gabashin kasar Syria, lokacin da suka yi kokarin cafke shi, bayan musayar wuta tsakanin sassan biyu.
Rahotanni sun nuna cewa, baya ga jagorantar ayyukan soja a kungiyar ta IS, a daya bangaren Abu Sayyaf, ya na da hannu cikin cinikayyar man fetur da iskar gas, da kuma hada-hadar kudade ta haramtacciyar hanya.
Minista Carter ya kara da cewa, sojojin na Amurka sun kuma cafke matar Sayyaf mai suna Umm Sayyaf, wadda itama ake zargin mai yiwuwa ta na da alaka kwarai da ayyukan ta'addanci da kungiyar IS ke gudanarwa.(Fatima)