in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Iraki na ci gaba da dakile sauran dakarun kungiyar IS a birnin Tikriti
2015-04-02 15:41:13 cri

Wani babban Jami'in kasar Iraki ya bayyana cewa, bayan da aka 'yantar da Tikriti, babban birnin jihar Salahudin dake arewacin kasar a Talata, sojojin kasar na ci gaba da dakile sauran dakarun kungiyar IS a birnin.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Mohammed al-Ghabban ya gaya wa manema labaru a wannan rana a birnin Tikriti cewa, wata rundunar soja ta Iraki na kai farmaki ga sansani na karshe na kungiyar IS a arewacin birnin, kuma za a dakile wadannan dakaru a cikin wasu awoyi. Mr. Ghabban ya kara da cewa, sojoji da 'yan sanda na kasar Iraki na kokarin kawar da abubuwa masu fashewa da dakarun IS suka bibbinne, inda hukumar 'yan sanda ta birnin za ta sake daukar nauyin kiyaye zaman lafiya bayan da suka kawar da dukkan nakiyoyin, kuma za ta kafa wani kwamiti mai kula da aikin karbar 'yan gudun hijira.

Ban da haka kuma, a wani labarin na daban, kungiyar tallafi da MDD ta tura wa kasar Iraki ta bayar da sanarwar cewa, a watan Maris na wannan shekara, rikici da farmaki da suka faru a kasar Iraki(ban da jihar al-Anbar) sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 997, a yayin da mutane 2172 suka ji rauni, kuma wadanda suka mutu sun hada da fararen hula 729 da sojoji 268. Sanarwar ta ce, wannan adadin mutuwa da raunatar mutane ya shafi lamarin da aka iya kidayawa kawai, watakila, hakikanin adadin zai fi haka.

Manzon musamman mai kula da batun Iraki na sakataren MDD kuma shugaban kungiyar tallafi da MDD ta tura ma kasar Jan Kubis ya bayyana a cikin sanarwarsa cewa, an yi mamaki ganin yawan mutuwa da raunatar mutane a sakamakon tarzomar da aka ta da a kasar Iraki, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta yi iyakacin kokari wajen kare rayukan fararen hula.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China