Sanarwar ta kuma jaddada cewa, tilas ne a ci gaba da daukar matakan kawo karshen kungiyar IS, da kawar da tsattsauran ra'ayinta na tada hankula, tare da gurfanar da masu hannu cikin ayyukan ta'addanci a gaban kotu.
Kwamitin sulhun ya yi kira ga dukkan kasashen duniya da su bi dokokin kasa da kasa, da kudurin kwamitin sulhun game da wannan batu, da yin hadin gwiwa tare da kasashen Libya da Habasha.
Hakazalika kuma, kwamitin sulhun ya bukaci kungiyar IS, da kungiyoyin dake da nasaba da Al-Qaida, da su saki dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su nan take ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Zainab)