in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Masar sun halaka masu tsattauran ra'ayi 36
2015-07-05 14:22:32 cri
Jiya Asabar 4 ga wata, wani jami'in hukumar tsaron Masar ya gaskata cewa, rundunar sojan kasar ta kai hare-haren sama kan wasu sansanonin dake hannun masu tsattsauran ra'ayi kuma ke arewacin lardin Sinai a ran 3 ga wata da dare, inda gaba daya suka halaka dakaru guda 36.

Bisa labarin da aka samu, an ce, dakarun magoyon bayan kungiyar Ansar Bayt al-Maqdis ne da suka bada yardarsu ga kungiayr IS.

Haka kuma, a wannan rana, shugaban kasar Masar Abdelfattah al Sisi ya kai ziyara ba zata a arewacin lardin Sinai, inda ya kai ziyara ga rundunonin sojoji da 'yan sanda da aka jibge wurin, ya kuma sa kaimi ga jami'an tsaron dake yaki da ta'addanci cewa, suna gudanar da aiki mai girma wajen kiyaye tsaron kasar.

A ran 1 ga watan Yuli, an kai harin ta'addanci mai tsanani a arewacin lardin Sinai a kasar Masar, inda 'yan bindiga suka kai hare-hare kan tashoshin gudanar da binciken soja a dama a wurin, inda kuma daga bisani kungiyar Ansar Bayt al-Maqdis ta sanar da daukar alhakin wadannan hare-hare . (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China