in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakile farmakin da kungiyar IS ta shirya kaddamarwa a Iraqi
2015-04-10 16:52:48 cri
Mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden yace, matakin soji da Amurka ta dauka a kasar Iraqi,ya taimaka wajen dakile harin da mayakan kungiyar IS suka shirya kaddamarwa, matakin da ke nuna cewa za a iya murkushe kungiyarta masu tsattsauranra'ayi.

Biden wanda ya bayyana hakan a jiyaAlhamis,yayin da yake jawabi gajami'an tsaron Amurka, yace a watanni 8 da sukagabata, kungiyar IS ta kaddamar da farmaki a sassa daban daban na kasar Iraqi, amma a yanzu wannan kungiya ta rasa yankuna da dama da a baya ta mamaye, inda a yanzu aka samu nasarar sauya halin da akeciki a kasar.

A mako mai zuwa ne dai firaministankasar Iraqi Haider al-Abadi,zai kai ziyara kasarAmurka, inda zai gana da shugabankasarAmurka Barack Obama.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China