in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kashe mutane kimanin 80 a Najeriya
2015-09-01 10:32:12 cri

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram, ta hallaka mutane kimanin 80 a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar Guardian ta Najeriya ce ta bayyana hakan, tana mai cewa a daren ranar 28 ga watan Agusta, mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani kauye dake jihar Borno, inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi, tare da hallaka fararen hula dake kokarin tsarewa farmakin, lamarin da ya janyi hallaka mutane 68.

A kuma ranar 29 ga watan na Agusta, 'yan bindigar sun harbe wani basarake da dan sa, da kuma makwabtansa su biyu a wani kauye. Har wa yau, a ranar 30 ga wannan wata, mayakan na Boko Haram sun harbe wasu kauyawa su 7, tare da jikkata wasu mutane 5, kamar dai yadda jaridar ta bayyana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China