in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani Basine ya samu sarautar gargajiya a Najeriya
2015-08-17 19:22:37 cri

A jiyan ne sarkin yankin Ikorodu da ke jihar Lagos a tarayyar Najeriya, Oba Kabir Adewale Shotobi ya baiwa manajan darektan kamfanin gine-gine na CCECC na kasar Sin da ke Najeriya Li Qingyong sarautar gargajiya ta Bobasona na yankin Ikorodu.

Oba kabir ya ce, ya yanke shawarar baiwa manaja Li sarautar ce saboda gagarumar gudummawar da shi kansa da kuma kamfanin na CCECC suka bayar wajen gina hanyoyi da kuma ci gaban yankin baki daya.

A jawabinsa na karbar sarautar yayin bikin da ya samu manyan baki, Li Qingyong ya ce, kamfanin CCECC zai ci gaba da samar da guraben ayyukan yi dubban 'yan Najeriya, baya ga fasahohi ga ma'aikatan da ke gudanar da ayyuka daban-daban a kasar.

A watan Nuwamban shekarar 2014 ne kamfanin ya kammala aikin gina babbar hanyar nan mai tsawon kilomita 12 da ta hade Lagos da yankin Ikorodu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China