in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 48 sun halaka a wata kasuwa a arewacin Najeriya
2015-08-12 09:25:44 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 48 ne suka halaka, yayin da wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a kasuwar Sabon Gari da ke yankin Danboa na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaye sunanta ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, sama da mutane 40 kuma sun ji munanan raunuka sakamakon fashewar bam din da aka zaton an dasa shi ne a cikin kasuwar.

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Idrissa Saleh ya ce, lamarin ya girgizar mazauna yankin, ganin yadda mutane da dama suka halaka.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance game da wannan hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China