Mista Ban ya bayyana hakan ne a sakon da ya gabatar ta hannun mai Magana da yawunsa Stephane Dujarric, inda ya ce babu dalilin da zai sa a kashe rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
A kalla mutane 48 ne suka hallaka a harin bomb na ranar Talatar nan a kasuwar Damboa dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria.
Mista Dujarric ya ce sakataren na MDD ya jaddada aniyar sa na bada dukkanin goyon baya kuma kwamitin MDD a shirye yake ya hada kai da gwamnatin Nigeria domin yakar ayyukan ta'addanci, wanda ya yi dai dai da tsarin dokokin 'yancin dan adam da na 'yan gudun hijira da kuma na jin kai na duniya.
Sai dai har yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar nauyin wannan harin. (Ahmad)