Kakakin shugaban Najeriya, Garba Shehu, ya bayyana ma manema labarai cewa kwamitin da aka dora wa nauyin wannan aiki na karbo dukiyar kasa da ke hannun tsoffin shugabannin siyasa na kasar zai fara aiki ba da jimawa ba.
Wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka na cikin tsarin manufar karbo dukkan dukiyar kasa da aka sace a Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a Afrika, da kuma kamfen gama gari na yaki da cin hanci, in ji mista Shehu.
Duk da haka, kamfen yaki da cin hanci da rashawa na shugaba Buhari da kuma matakinsa na rage cin hanci sosai a Najeriya na iyar fuskantar tirjiya daga wasu mutanen kasar a matsayin wani bi ta da kulli, maimakon wani aikin da zai taimaka wa kasar.
A cewar wani mai fashin bakin siyasa, Yinka Fayomade, kamfen shugaban Najeriya na yaki da cin hanci, wasu na daukar sa tamkar wani abin da ya riga ya rasa tagomashi wanda kuma aka juya akalarsa kan manyan masu yi ma shugaba Buhari adawa.
Jam'iyyar APC da ke mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP sun shiga cikin sabanin ra'ayi kan batun yaki da cikin hanci. (Maman Ada)