Wani mutun ne dai ya kai harin lokacin da ya kwance bam din dake jikin shi a dai dai kofar shiga kasuwar kamar yadda kakakin 'yan sandar jihar Aderemi Opadokun ya tabbatar ma wakilin Xinhua.
A cewar rundunar 'yan sandan da gani mutumin ya yi nufin kai ma wani sansanin jami'an tsaro ne dake bakin kasuwar sai dai hakan bai yiwu ba.
Tuni dai aka kwashe buragujin gawar dan kunar bakin waken da sauran mutane 3 da harin ya rutsa da su zuwa asibitin gwamnati dake garin Uba sannan wadanda suka ji rauni suna karban jinya. Harin kunar bakin wake da yawancin 'yan kungiyar Boko Haram suke kaiwa tun daga shekara ta 2009 ya yi sanadiyar rayuwar dubban jama'a a wannan yankin a Nigeriya.
Karuwan hare haren na baya bayan nan ya biyo turjiya da kungiyar ke nuna wa akan sabon gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda tun bayan hayewar shi mulki ya zuwa yanzu akalla kusan mutane 800 sun rasa rayukan su. (Fatimah)