in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeriya sun kama wadansu da ake zargi da halaka sojojin kasar
2015-08-11 11:12:41 cri
Dakarun Nigeriya da ke yankin Niger Delta mai arzikin man fetur sun tabbatar da kame wadansu da mutane 6 da ake zargi 'yan fashin teku ne da hannun a kisan sojoji 4 da dan sanda 1 a wani harin da aka kai kan sansanin sojojin.

Kakakin sojojin Isa Ado ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, dakarun sun kaddamar da samame ne a sansanonin mayakan da ke dauke da makamai da ke yankin Degema inda suka yi nasarar kame maza 4 da mata biyun da ake zargin.

Kakakin ya kuma tabbatar da cewa, dakarun sun yi nasarar gano dimbin makamai da harsasai a lokacin wannan samamen, kuma yanzu haka sojiojin suna farautar ragowar maharani da suka tsere.

Rundunar 'yan sandan yankin ta tabbatar da cewa 'yan fashin tekun da ake zargi da wannan aika aika dai sun kai hari kan sansanin sojin yankin Nembe dake jihar Bayelsa ne a daren ranar jumma'a.

A 'yan shekarun baya-bayan nan ana kara samun karuwar ayyukan fashin teku da fashi da makami a kan ruwan Nigeriya lamarin da ya janyo hankalin sauran kasashen duniya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China