in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na neman wata mafita kan takunkumin EU kan kayayyakin nomanta
2015-08-08 13:40:31 cri
Kasar Najeriya za ta yi iyakacin kokarinta domin jirkice takunkumin da tarayyar Turai EU ta kakaba mata kan kayayyakin nomanta a makon da ya gabata, in ji majalisar dattawan kasar a ranar Jumma'a.

A cikin wata sanarwa, shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya tabbatar da cewa wani kuduri kan hana fitar da kayayyakin abinci an tabo maganarsa a ranar Alhamis bisa kuma ana kokarin neman wata mafita kan wannan takunkumi na tarayyar EU kan kayayyakin gona da ke fitowa daga Najeriya har zuwa shekara mai zuwa.

Shugaban majilsar dattawan ya yi kira ga hukumomin daidaita harkoki da abin ya sha da su dauki nauyin da bisa wuyansu da kuma yin aiki tukuru domin ganin an kaucewa wannan hani tun da wuri.

Hukumar tsaron abinci ta tarayyar Turai ta bayyana cewa, wasu kayayyakin abinci da ke fitowa daga Najeriya suna dauke da wasu sinadarai masu guba da ba a amince da su ba, a lokacin da ta bayyana daukar wannan mataki a makon da ya gabata.

Kayayyakin abincin da wannan mataki ya shafa sun hada da 'ya'yan gunar melon, busasshen kifi da nama, ridi, wake, man kwakwa da gyada da sauransu.

Wannan takunkumi zai iya kawo sakamako maras kyau ga tattalin arzikin Najeriya, da yanzu haka yake mafi girma a nahiyar Afrika, in ji masu fashin baki a fannin tattalin arziki na kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China