in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasa na musamman na Nigeriya sun samu yabon Shugaban kasa
2015-08-11 10:23:52 cri
'Yan wasa na musamman na kasar Nigeriya a ranar Litinin din nan suka samu yabo daga shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda ya jinjina ma irin kokarinsu a wasanin duniya ta musamman da aka kammala kwanan nan a kasar Amurka.

A cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, shugaban ya bayyana nasarar tawagar da wani mai kara kwarin gwiwwa ganin yadda suka lashe kyautuka 71, ciki har da zinarai 34.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar ma 'yan wasan cewa gwamnatin tarayya a daukan 'yan Nigeriya sun yi alfahari da wannan kokari nasu da bajinta a lokacin wasannin wanda suka lashe wadannan lambobin yabo a duk wasanni da suka yi.

Sanarwa wadda kakakin fadar gwamnati Malam Garba Shehu ya sanya ma hannu ta kuma ce shugaban kasar ta Nigeriya ya yi alkawarin cewa da kansa zai karbi tawagar a fadarsa domin taya su murna. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China