in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya yayi kiran da a kawo karshen Boko Haram nan da watanni uku
2015-08-14 11:03:31 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin sojojin kasar a ranar Alhamis da su kawo karshen boren kungiyar Boko Haram, da ma sauran matsalolin tsaro da kasar take fuskanta nan da watannin uku masu zuwa.

Mista Buhari, yayi wannan kira a lokacin da yake baiwa sabbin shugabannin sojoji lambar yabo a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, inda ya bayyana cewa fashi da makami, sace sacen mutane da kaifin kishin addini bisa nau'o'i daban daban da kuma wasu kalubalolin tsaro sun zama dole a rage sosai kafin watan Satumba.

Illar yawaitar hare hare da lalata gine gine da mayakan kungiyar suke yi sun sanya gwamnatin Najeriya daukar matakai daban daban bisa burin dakatar da ayyukansu da kuma maido da doka da oda a yankunan kasar baki daya, in ji shugaba Buhari tare da jinjinawa kokarin rundunonin kasar kan yakin da suke da Boko Haram.

Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar sojojin Najeriya da ta cigaba da aiki tare da sauran bangarori daban daban masu ruwa da tsaki domin bullo da wani shirin hadin gwiwa bisa tsari da zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram da sauran manya laifuffuka a cikin kasar.

Shugaban tsaron kasa, Laftana janar Abayomi Olonishakin ya shaida wa manema labarai cewa shi tare da sauran shugabannin soja suna aiki na neman dabarun yadda za a fuskanci matsalolin tsaro a Najeriya.

Shugaban kasa ya bada umurni, don haka za a yi iyakacin kokari domin biyan bukatarsa, in ji mista Olonishakin.

Shugaba Buhari ya nada sabbin shugabannin sojojin Najeriya a cikin watan da ya gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China