A lokacin ziyarar tashi, magatakardan zai gana da gwamnonin jihohin kasar 36 karkashin taken "samar da hanya ma sabuwar Najeriya: matsayi na gwamnatocin en'e-en'e", in ji bayanin da ke kunshe a sanarwar ma'aikatar harkokin wajen.
Babban jami'in majalissar har ila yau zai aiwatar da bikin saka fure domin juyayin shekaru hudu na harin bam din da aka kai a ofishin majalissar dake Abuja, sannan zai aiwatar da sauran ziyarce-ziyarcen aikin shi.
Bayan haka akwai wassu tattaunawa biyu a kan tattalin arziki da demokradiya a Najeriya wanda ake sa ran Mr Ban zai halarta. Muhimmin abin da zai yi lokacin ziyarar shi ne ganawa da Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, wadanda suka gana a baya lokacin taron G7 na kwanan nan a kasar Jamus.
Shugaban na Najeriya da Babban magatakardan MDD za su kira taron manema labarai tare bayan ganawar tasu, in ji ma'aikatar harkokin wajen Nigeriya. (Fatimah Jibril)