Najeriya ta nuna rashin jin dadinta game da tuso keyar 'yan kasarta fiye da dubu 12 da hukumomin kasar Kamaru suka yi a baya bayan nan, tare da bayyana cewa korar ta sanya wadanda lamarin ya shafa cikin wani mawuyacin hali da suka saba wa hakkin dan adam.
Hukumomin na Najeriya sun bayyana cewa yawancin mutanen da aka maido kasarsu 'yan gudun hijira ne da suka yi fama da hare haren Boko Haram sau da dama, hukumar kula da bala'u da bada agajin gaggawa ta NEMA, dake daukar nauyin mutanen da matsalar ta shafa, ta soki kasar Kamaru da rashin sanar da wannan mataki nata tun da wuri.
Dalilin haka ne, gwamnatin Najeriya ta sanar da ayyukan Kamaru ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) domin nazari kan wannan batun, in ji babban darektan NEMA, Sani Sidi a gaban 'yan jarida a ranar Talata.
Ya kuma kara da cewa, "mun bayyana korafe korafen mu ga shugabannin HCR, ta nuna cewa idan da Najeriya ce ta aikata irin wadannan ayyuka ga kasar Kamaru, da tuni HCR ta soki kasar mu, amma duk da haka ba mu ce kome ba, muka yi shiru kan wadannan ayyuka na gwamnatin Kamaru", Jami'in ya ce, har yanzu yana jiran ya ga matakin da ya dace da hukumar HCR za ta dauka kan wannan batu.
Mutanen da aka koro daga kasar Kamaru, yanzu haka suna yankin Mubi a jihar Adamawa dake arewa maso yammacin kasar, kuma za'a kwashe su zuwa sansanonin da tuni aka kafa domin karbarsu bayan an kammala aikin binciken lafiyarsu da kuma tantace su. (Maman Ada)