in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yobe: An hallaka mutane 5 a harin kunar bakin wake
2015-08-25 19:23:18 cri
A kalla mutane 5 ne suka rasa rayukan su, yayin wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Damaturun jihar Yobe, dake arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun ce wata 'yar kunar bakin wake 'yar kimanin shekaru 14 ce ta tashi Bam din dake jikin ta a kofar wata tashar mota dake birnin da safiyar Talatar nan. An ce baya ga wadanda suka rasu wasu mutanen kusan 25 sun jikkata.

Tuni dai ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta tabbatar da aukuwar wannan lamari. NEMA ta ce wadanda suka samu raunuka na samun kulawar jami'an lafiya a babban asibitin birnin na Damaturu. Wani ganau mai suna Aminu Usman, ya ce tun da fari 'yar kunar bakin waken ta yi kokarin shiga tashar motar amma jami'an tsaro suka hana ta, daga bisani ne kuma ta doshi wata karamar motar fasinja dake shirin fitowa daga tashar, ta kuma tashi Bam din dake jikin ta, lamarin da ya janyo rasuwar fasinjojin dake cikin motar, baya ga ita kanta 'yar kunar bakin waken.

Wannan harin dai na zuwa ne kasa da kwana guda, bayan da babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya kammala ziyarar aiki a Najeriyar, inda ya yi kira da a kara azamar kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, koda yake ana danganta irin wannan hare-hare da kungiyar Boko Haram. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China