A kwanan baya MDD ta yi bikin baiwa rukunin aikin wanzar da zaman lafiya zagaye na 13 da Sin ta tura wa kasar Sudan ta kudu lambobin yabo.
Yayin bikin, babban kwamandan tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta kudu ko UNMISS a takaice, ya jinjinawa ayyukan da sojojin Sin suke yi, tare da baiwa rukunonin injiniyoyi, da na masu aikin jiyya, da wasu nagartattun sojoji lambobin yabo na musamman bisa gudunmawar su.
A cikin jawabin da wannan babban kwamandan ya gabatar, ya bayyana cewa rukunin kasar Sin na da da'ar aiki, yana kuma da ba da hidima mai inganci, ya kuma samar da ci gaba mai armashi.
Bisa labarin da aka bayar, an ce rukunin sojoji injiniyoyi na kasar Sin, bisa umurnin tawagar UNMISS, ya tura sojoji zuwa jihar Unity, inda suka sake bude hanyar da aka katse kusan shekaru 2, haka nan ayarin motocin dake aikin jin kai na MDD, sun isa yankin arewacin kasar, aikin da ya zamo mai babbar ma'ana wajen tabbatar da lafiyar fararen hula, da kuma tsimin kudi ga tawagar.
Rukunin Sin a karo na 13 ya kunshi sojoji 331, da suka hada da jami'ai 112 wadanda suka taba gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen waje sama da sau biyu. Yayin da suke gudanar da ayyukansu a Sudan ta kudu, jami'an da aka girke a birnin Wau hedkwatar jihar West Bahr-al-Ghazal, sun taka rawar gani game da ayyukan gyara, da kiyaye hanhoyi, da filayen saukar jiragen sama, da na'urorin samar da wutar lantarki da ruwa, da kuma kawar da makamai da sauransu. (Amina)