Rahotanni dai na cewa ana ci gaba da shawarwari a birnin Adis Ababan kasar Habasha tsakanin masu ruwa, inda a jiya Lahadi Machar ya yi ganawar sirri da shugaba Omar al-Bashir na Sudan, karkashin shirin shiga tsakanin da kungiyar bunkasa Gabashin Afirka ta IGAD ke jagoranta.
Yayin ganawar tasu Machar ya shaidawa shugaba Al-Bashir cewa, bangaren sa ya fi bukatar ganawar kai tsaye, sai dai kungiyar IGAD ta nace kan tattaunawa da dukkanin masu ruwa da tsaki. Mr. Machar ya kara da cewa, cikin tattaunawar da ake yi yanzu haka, ba a kai ga tabo tushen batutuwan da ake kace-nace a kan su ba.
Kaza lika mataimakin tsohon shugaban kasar Sudan ta Kudun ya bukaci da a cimma wata yarjejeniya tukuna, kafin kafa gwamnatin rikon kwarya, matakin da a cewarsa zai basu damar shiga a dama da su, wajen aiwatar da manufofin gwamnatin ta riko.